1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sace ma'aikatan jirgin ruwa a gabar Najeriya

Gazali Abdou Tasawa
July 2, 2020

Wasu 'yan fashin teku sun kai farmaki a wannan Alhamis kan wani jirgin ruwan kasar Norway a gabar ruwan Najeriya inda suka sace ma'aikatan jirgin su tara dukkansu 'yan Najeriya.

https://p.dw.com/p/3eiQF
Brasilien Cidade de Sao Mateus Explosion auf Ölplattform
Hoto: picture alliance/Demotix

Kamfanin BW Offshore da ke aikin hakar man fetur, da kuma jigilarsa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis inda ya ce maharan sun kai farmaki ne a kan jirgin ruwan mai suna Senje Berge a kusa da cibiyar mai ta Okwori da misalin karfe hudu da minti 20 wato uku da minti 20 agogon JMT.

 Kawo yanzu dai ba a da duriyar ma'aikatan jirgin da aka sace da kuma halin da suke ciki. Sai dai kamfanin na BW Offshore ya ce yana tattaunawa da mahukuntan Najeriya kan batun jirgin wanda ke yi wa kamfanin Addax Petrolium na kasar Chaina aiki a lokacin da 'yan fashin tekun suka fal masa.