1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun kashe mutum 17 a Zamfara

Ramatu Garba Baba
December 24, 2018

Mutum akalla 17 ne suka mutu a sanadiyar wasu sabbin hare-hare da 'yan bindiga suka kai a wasu kauyuka da ke a jahar Zamfara a arewacin Najeriya a karshen mako.

https://p.dw.com/p/3AauC
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Shedun gani da ido sun fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa,  maharan sun kutsa cikin kauyen Magami akan babura, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi. Daya daga cikinsu mai suna Kasimu Bello ya ce bayan harin sun kwashi gawarwaki goma sha bakwai da suka yi wa jana'iza.

Kakakin gwamnatin jahar, Mohammed Shehu, ya ce sun soma bincike, kuma za su yi duk mai yiyuwa don gano wadanda suka aikata kisan. Kafin wannan harin na ranar Asabar da ta gabata ma dai, an kai wani hari a ranar Laraba na makon jiya inda mutane ashirin da biyar suka rasa rayukansu.