1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin albashi ya janyo yajin aiki a Najeriya

Ramatu Garba Baba
September 14, 2020

Jami'an kiwon lafiya a sassan Najeriya ne suka soma yajin aiki a wannan Litinin bayan da suka baiyana rashin amincewa da rashin biyansu albashi da kayayyakin kare kansu daga cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3iRxF
Simbabwe Streik der Ärzte
Hoto: AFP/J. Njikizana

Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya sun tsunduma yajin aiki a wannan Litinin kan batun kin biyansu albashi da kuma zargin kin cika musu alkawura da gwamnatin ta dauka na biyansu wasu alawus a aikin yakar annobar Coronavirus dama kayayyakin da suke bukata don kare kansu daga cutar.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar likitocin, ya ce, sun dauki matakin ne bayan da suka gagara cimma matsaya da bangaren gwamnati duk da cewa gwamnati ce ta yi alkwarin yi musu karin kudin alawu-alawus dama karin kudin albashi a tsawon lokacin da za su dauka a yakar annobar.

Masana dai, sun baiyana damuwa kan halin da za a tsinci kai, muddun ba a yi kokarin shawo kan wannan matsalar ba, ta la'akari da yadda cutar ke ci gaba da yaduwa a Najeriyar. Mutum sama da dubu hamsin ne suka kamu da cutar Corona a kasar ciki har da jami'an kiwon lafiya dubu daya.