1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudun auren mata masu kaki a Najeriya

January 24, 2023

Matan da ke sanya kaki da kayan sarki a Najeriya, na samun matsala wajen samun matasa da sauran al'umman da ke tunkararsu da sunan neman aure saboda fargabar abin da ka je ya zo.

https://p.dw.com/p/4MeWG
Mata | 'Yan Sanda
Ko a wasu kasashen matan da ke saka kaki ko kayan sarki na fuskantar kalubale?Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Koda yake ba kowa ne ke nuna irin wannan fargabar ba, amma mafi akasari ana samun matsalar auren matan da suka kasance sojoji ko 'yan sanda ko kuma yin wani aiki da ake saka kaki ko kayan sarki. Duk da wannan fargaba dai, ana samun matasan da kan tinkari irin wadannan mata, koda yake wasu na ganin matan ba za su dauki wasa da hankali ba. A nasu bangaren, matan na ganin ba su da wata wahalar tunkara, in dai har mutum da gaske yake to suma a shirye suke da su saurare shi. Wasu dai da Dw ta zanta da su, sun bayana cewa ba za su iya soyayya da irin wadannan matan ba, koda yake wani ya ce ya taba yin soyayyar da mai saka kayan sarkin kafin ya janye daga bisani.