Najeriya ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka | Siyasa | DW | 07.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka

Najeriya ta sake alkaluma da ke bayani kan tattalin arzikin kasar wadanda suka nuna girman tattalin arzikin kasar ya zama mafi girma tsakanin kasashen Afirka baki daya.

Najeriya ta fitar da sabon alkaluman auna mizanin tattalin arziki da ya nuna cewar tattalin arzikin Najeriyar ya zabura inda a yanzu ya zama na daya a Afrika kuma kasar ta zarta Afrika ta kudu, to sai dai ana nuna damuwar yadda ba'a ga wannan ci gaba a fanin rayuwar talakan kasar ba.

To fitar da sabbin alkaluman auna mizanin tattalin arziki da hukumar kula da ofishin kididigan kasar ya yi bayan kwashe fiye da shekaru 24 ya nuna cewa Najeriyar ce ke da tattalin arziki mafi girma a Afrika inda take da mizanin na auna arzikin kasa na GDP da ya kai dalla bilyan 509.9 abin da ya bata ikon zama kasa ta 26 mai karfin atttalin arziki a duniya, inda ya nuna ta samu ci gaba da matsayi goma.

Ambassada Bashir Yuguda shi ne minister mai kula da ma'aikatar tsare-tsaren kasa a Najeriyar, ya bayyana abin da wannan ci gaba ke nunawa ga Najeriyar.

"Abin da ya fito cikin wannan shi ne ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya a yanzu ba ya dogara ne a kan man fetir ba , an samu ci gaba wasu fanonin na daban Kaman aikin gona, Kaman sabon fanin nan da ake yi fina-finai da kuma hanyoyi na ci gaban yau da kullum na jama'a."

Nigeria Finanzminister Ngozi Okonjo-Iweala

Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala

Koda yake Najeriyar tana dokin kaiwa ga wannan matsayi na tsere Afrika ta kudu a karfin tattalin arziki, amma fa ministar kula da harkokin tattalin arzikin Najeriyar Dr Ngozi Okonjo Iweala ta ce akwai sauran aiki a gaba.

Ta ce "Duk da cewa mizanin tattalin arzikinmu na da girma a Afrika da duniya, to amma in aka kwatanta da mizanin ga kowane dan Najeriya to kasar ta zamo ta 121 a duniya saboda haka kada wannan ya dauke mana hankali."

An dai fitar da wannan ci gaban na Najeriya ne a dai dai lokacin da Bakin Duniya ya sanya Najeriya a jerin kasashen da suka fi fama da matsanancin talauci a duniya, abin da ya sanya kwararru tambayar shin me yasa babu alaka a tsakanin wannan ci gaba na tattalin arzikin Najeriya da rayuwar talakan kasar da a kullum ke koken bai gani a kasa ba. Ko menene gaskiyar wannan? Har ita yau ga minsita Bashir Yuguda.

"Wannan gaskiya ne don wannan yana daya daga cikin muhimmancin wannan aikin da aka yi domin a duba hanyoyin da za'a tabbatara da talaka shima ya shaidar da wannan ci gaba na tattalin arziki da aka samu domin a rage wa jama'a matsaloli da ake da su na yau da kullum."

Shekaru 24 ke nan rabon Najeriya da ta sake tsara maunin tattalin arzikinta, abin da mahukuntan kasar ke fatan zai sake zaburara da tattalin arzikin kasar kamar yadda ya faru a wasu kasashen duniya irin na Ghana.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Suleiman Babayo/Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin