1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma aikin rijistar baki a Najeriya

Uwais Abubakar Idris GAT
July 15, 2019

A Najeriya hukumar kula da shigi da ficen jama’a ta fara aikin rijistar bakin ‘yan kasashen waje da ke zama da ya wuce watani uku a kasar a matakin kara samar da cikakken tsaro.

https://p.dw.com/p/3M6Xn
Ausländer Verhaftungen in Kano Nigeria
Hoto: DW

Aikin rijistar bakin ‘yan kasashen waje kama daga wadanda suka fito daga kasashen yankin Afrika ta Yamma ya zuwa na nahiyar Turai da ma Asiya, an tsara shi ne domin Najeriyar ta san yawan bakin da ke zaune a kasar a mataki na kyautata al’amuran tsaro. Aikin wanda rabon da a yi irinsa a kasar tun shekarun 1980 da ya kai ga korar wasu ‘yan kasashen ketare.

Ausländer Verhaftungen in Kano Nigeria
Jami'in shigi da Ficen Najeriya na fira da 'yan jarida kan aikin rijistar bakiHoto: DW

Tuni dai ‘yan kasashen waje da suka hada da ‘yan kasashen Sin da wasu ‘yan yankin Afrika ta Yamma suka fara yin rijista wanda aka ba da wa’adin watanni shida ana yinsa, gwamnatin Najeriyar ta yi sasauci ga wadanda suke zaune a kasar ba bisa doka ba in suka yi rijistar an yafe masu. Najeriya dai kasa ce da ke fama da matsaloli na rashin tsaro da akan danganta su da batun bakin haure da kan shigo kasar ta hanyoyi da dama, wannan na cikin muhimmin dalili na sanin zahirin yawan mutanen da ke zaune a kasar. 


A baya dai an nuna tsoron amfani da rijistan domin cin zarafi ko korar baki kamar yadda ta taba faruwa a shekarun 1980 a Najeriyar. Abin jira a gani shi ne tasirin da wannan aiki zai yi a wajen kyautata yanayin tsaro a kasar.