1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta shirya kare hakkin majinyata daga yanzu

July 31, 2018

A kokarita na sauya tsarin kiwon lafiya a Najeriya, gwamnatin kasar ta kaddamar da sabon tsarin kare hakkin marasa lafiya a asibitocin kasar.

https://p.dw.com/p/32P7Z
Nigeria | Krankenhaus in Abuja
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Karkashin wani kundin da gwamnatin tarrayar Najeriyar ta kaddamar a Abuja dai daga yanzu wajibi ne ga duk wani mai bukatar kulawar gaggawa da ya samu kulawar kafin fara kai wa ga batun biyan kudi ko dai a asibitoci na gwamnati ko kuma masu zaman kansu cikin tarrayar Najeriya.

Nigeria Anschlag in Gombe
Hoto: picture-alliance/dpa

Sabon kundin har ila yau ya tanadi samar da cikkakkun bayanai ga marasa lafiya a cikin hali na aminci ga daukacin nau’in cutar da ta ke damunsu da kuma irin tsarin maganin da ake shirin dora shi a kai. Ko bayan nan dai tun daga yanzu dole ne a sanar da maras lafiya yawan kudin da ya ke bukata kafin kaiwa ga fara bashi magani na cutar da ke neman warkarwa.

Karin kisan kudin da ke shirin zuwa harkar ta lafiya dai na iya kaiwa ga samun inganci na abin da ke iya fitowa a cikin filin daga na lafiya. Wannan filin daga kuma ya kunshi huldar da ake gudanarwa a tsakanin masu neman lafiya da kuma masu sana’ar kiwonta.

DW_Delta8
Hoto: Katrin Gänsler

Babban burin kundin dai a fadar mataimaki na shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo shi ne iya kaiwa ga karin inganci ga harkar ta lafiya da sannu a hankali ke daukar hankalin mahukunta. Abin jira a gani dai shi ne iya kaiwa ga aiwatar da sauya tsohuwar al’adar da ke zaman jini a cikin tsoka na lokaci mai nisa ga masu bada lafiyar cikin tarrayar Najeriyar.