Najeriya ta shawo kan cutar Polio | Siyasa | DW | 10.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta shawo kan cutar Polio

Tun kusan shekarar 1988 ne dai Tarrayar Najeriya ta fara kokari na yakar cutar shan inna, amma sai a bana ne ta fara hango hasken kai karshen cutar ta shan inna.

An dai kira sunan kokari na kare wani dangi, an ma rada mata tagomashin addini, to sai dai kuma Tarrayar Najeriya na shirin yin nasara kan cutar shan inna bayan share shekara guda babu rahoton bullarta cikin kasar. Duk da cewar dai tun a shekarar 1988 ne dai kasar ta fara shiri na ganin bayan cutar, shekaru kusan takwas can baya na zaman mafi zafi a cikin yakin da ya kalli sallo da nau'in addini, ya ma nemi fito na fito a tsakanin sassa daban daban cikin kasar.

Alal misali dai, ko bayan adawar fatar bakin da ta kai har ga barazanar yin dauri, masu allurar rigakafin shan innar sun kai har ga asara ta rayuwa sakamakon harin da aka kai musu shekaru biyu baya a biranen Kano da Maiduguri ta jihar Borno. Abun kuma da ya dauki hankali ciki da ma wajen kasar amma kuma ya sauya akalar yakin zuwa nasarar dake zaman irinta ta farko kan wata cuta a sama da shekaru 30 baya. Cikin kasa da tsawon makonni biyun dake tafe ne dai Najeriya ke cika shekara guda cur ba tare da rahoton bullar cutar a ko ina, kama daga yankin arewa maso gabas mai fama da ta'ddanci, ya zuwa dan uwansa na arewa maso yamma dake masa kallon kokari na kaiyyade yawan al'umma. Abun kuma da a idanun hukumar lafiya ta duniya ke zaman nasarar tsaida yaduwar cutar a kasa. Dr Ado Mohammed dai na zaman shugaban hukumar lafiya matakin farko ta kasar, kuma jagoran yakin da ya kalli tsoma bakin sarakuna da malaman addinai da nufin tunkarar matsalar.

Ko bayan nasarar shawo kan masu adawar da suka hada da masanan kimiyya da likitoci da malaman addinai dai, wata matsalar da shirin yai nasarar yaka na zaman ta ta'addancin da ta maida jihohin Borno da Yobe da Adamawa na ba shiga ga masu allurar shan innar. Kafin a fadar Dr Mohammed din jami'an hukumar sun dauki dabarar sari ka noken da tai nasarar hana yaduwar shan innar duk da barazana ta rayuka ga jami'ai na lafiya a jihohin.

Tuni dai aka fara tsallen murna kama daga jami'ai na lafiyar da suke kallon nasarar da babu irinta, ya zuwa sarakuna dama sauran masu ruwa da tsaki da batun shan innar cikin kasar. Musbahu Lawal Didi dai na zaman shugaban kungiyar masu dauke da cutar shan innar a kasar ta Najeriya, kuma farin ciki ya nuna babu misali a ganin karshen abun da kowa bai son barin gado ga na bayansa. To sai dai kuma sai a shekara ta 2017 ne dai kasar ke iya samun shaidar karshe daga hukumar ta duniya kan cutar da ta rage a kasashen Afganistan da Pakistan da kuma ita kanta kasar ta Najeriya kafin nasarar.

Sauti da bidiyo akan labarin