Najeriya ta soke rundunar SARS
October 11, 2020Talla
Wannan mataki ya biyo bayan jerin zanga-zanga mai zafi daga fitattun 'yan kasar a ciki da waje da kuma shafukan sada zumunta na neman a soke rundunar kan zargin yadda suke kashe rayukan mutane da dama.
A shekarar 1992 ce gwamnatin Najeriya ta kirkiro da sashin SARS domin yaki da masu fashi a kasar, sai dai tun bayan nan an wa rundunar kallo tana fakewa da kaki tana cin zarafin al'umma, zargin da rundunar ta ce babu gaskiya a cikinsa. An dai samu wasu kungiyoyi da ke neman a wanke rundunar daga dukkannin zargi da suka da suke sha daga kudancin kasar.