SiyasaAfirka
Najeriya ta kubutar da daliban Kebbi daga hannun yan bindiga
November 26, 2025
Talla
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da kubutar da daliban nan 24 'yan mata, na makarantar sakandaren Maga a jihar Kebbi, wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar 17 ga watan Nuwamba.
Kakakin shugaban Bayo Onanuga, ya ce ta hanyar laluma suka ceto 'yan matan, ba tare da wata hatsaniya ba.
Karin bayani:'Yan bindiga sun sake sace daliban Najeriya cikin mako guda
Shugaba Bola Tinubu ya alkawarta samar da karin jamai'an tsaro, domin magance afukuwar hakan a nan gaba, bayan da aka fuskanci hare-haren 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane kwanan nan a jere, a sassa daban-daban na kasar.