Najeriya ta kama hanyar samun 'yan sandan jiha
June 25, 2026
Haka dai ta kama hanyar cimma ruwa ga ‘yan Najeriyar da tun 1970 da aka hade rundunar 'yan sandan ta zama ta tarayya suke neman da a kafa ‘yan sanda na jihohi. Amincewa da kudurin doka da majalisar dottawan Najeriya ta yi bayan da bangaren shugaban kasar Bola Tinubu ya sake aikewa da majalisar da nasa tasri na dokar. Majalisar dottawan ta tsara cewa 'yan sandan na jihohi da za'a kafa za su yi aiki ne tare da ‘yan sandan tarayya da ake da su. Sanata Aliyu Ahmad Wadada dan majalisar dottawan Najeriyar ne ya yi min karin haske a kan abinda suka amince da shi.
"Yanayin da muke ciki a kasar nan yau, maganar ko wasu za su yi amfani da dama su yi amafani da ita, muna bukatar ‘Yan sandan jihohi don barazana da rashin zaman lafiya. Wanda duk ya karanta tarihi a lokacin da muke da ‘yan sanda na jihohi kowa ya san akwai doka''.
Tuni aka fara maida martani a kan wannan muhimmin sauyi da zai shafi yadda ake tafiyar da harkokin samar da tsaro a cikin al'umma, musamman a matakin jihohi. Dan majalisar dokokin kasar Amurka Riley Moore ya jinjinawa 'yan majalisar yana fatan cewa 'yan sandan jihohi za su taimaka samar da tsaro ga kiristoci domin a baya ya sha magana a kai. Farfesa Abdulkadir Suleiman Muhammad Malami a jami'ar Abuja ya ce akwai bukatar taka tsan-tsan.
Samun nasarar amincewa da kudurin doka na kafa ‘yan sandan jihohi wani babban sauyi ne na tsarin mulkin Najeriya da aka yi tun 1999 da Najeriyar ta koma bisa mulkin dimukuradiyya. A wannan sabon tsari ‘yan sanda jihohi su ne ke da hurumi na aiwatar da dokoki na jihohinsu na tabbatar da doka da oda da kare aikata miyagun laifuffuka. Akwai tsoron gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan wajen biyan bukatunsu na siyasa. 'Yan majalisar sun bada tabbacin daukar matakan da suka dace kamar yadda Sanata Aliyu Ahmad Wadada ya bayyana.
A yanzu kallo ya koma ga majalisun dokoki na jihohi domin sai an samu amincewa na kasha 2/3 na ‘yan majalisar kafin kudurin ya zama doka a kasar a Najeriya abinda zai sauya daukacin tsarin jami'an tsaro a kasar.