Najeriya ta fitar da bayanai kan tattalin arziki | Labarai | DW | 06.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta fitar da bayanai kan tattalin arziki

Najeriya ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka baki daya

Najeriya ta sake alkaluma da ke bayani kan tattalin arzikin kasar wadanda suka nuna girman tattalin arzikin kasar ya kai euro bilyan 510, mafi girma tsakanin kasashen Afirka baki daya.

A shekara ta 2012 karfin tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu bisa ma'auni ya nuna kimanin euro bilyan 384. Najeriya ta fitar da alkaluman bayan gudanar da sauye-sauye na saka bangarorin masu mahimmanci kamar sadarwa da ake da kimanin masu wayar hannu fiye da milyan 100, maimakon layukan tarho dubu 300 da ake da su cikin shekarun 1990, da sufurin jiragen sama, da sabbin kafofin sadarwa, da sauran fannoni. Amma duk da haka kimanin kashi 70 cikin 100 na al'umar kasar na rayuwa karkashin mizanin talauci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu