1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya na binciken dan sandanta Abba Kyari

July 30, 2021

'Yan sandan Najeriya sun fara bincike kan zargin da Amirka ke yi wa jami'insu DCP Abba Kyari bayan da kasurgumin mai damfara Ramos Abbas da ake wa lakabi da Hushpuppi ya yi zargin cewa ya taba ba Kyarin cin hanci.

https://p.dw.com/p/3yKcH
Nigeria Polizeikräfte in Lagos
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

A cikin wata sanarwa da Frank Mba mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya ya fitar ya ce rundunarsu ta dukufa wurin tabbatar da adalci, a don haka ta kaddamar da binciken.

A Najeriya dai ana yi wa Abba Kyari kallon mutunci a matsayin kwararren dan sanda da ya kasance dodon 'yan bindiga masu garkuwa da mutane. Kazalika masu aikata manyan laifuka a cikin birane ma na tsoron haduwa da Abba Kyarin ganin yadda ya jima yana samun galaba kan masu aikata laifuka musamman garkuwa da mutane. Tuni dai dan sandan ya musanta zargin da ake ma sa.