Najeriya ta bi sahun kasashe a yaki da sauyin yanayi | BATUTUWA | DW | 09.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya ta bi sahun kasashe a yaki da sauyin yanayi

Yayin da ake taron duniya kan sauyin yanayi a kasar Jamus, majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudurin dokar kafa hukumar kula da rage matsaloli na sauyin yanayi da suka sanya kasar a gaba.

A dai dai lokacin da ake gudanar da taron duniya kan sauyin yanayi a kasar Jamus, a Najeriya majalisar wakilan kasar ce ta amince da kudurin doka da ya tanadi kafa hukumar musamman da za ta kula da kudurorin rage matsaloli na sauyin yanayi da a zahiri suka taso al'ummar kasar a gaba.

Majalisar wakilan Najeriyar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan kara ta'azzarar da matsaloli na sauyin yanayi ke yi a kasar, domin kama daga gurbacewar muhalli a yankin Niger Delta zuwa ga zaizayar kasa da gurgusowar hamada da ke ci tamkar wutar daji a jihohi da dama a arewacin kasar, sai uwa uba a bana an ga yawaitar zafin rana da daukewar ruwa da wuri, abin da ya sanya manoma da dama tafka asara. Wannan ya tayar da hankalin ‘yan majalisar da suka  amince da dokar don neman tsira ga kasa da ma al'umma daga matsalolin sauyin yanayin.

Nigeria Ölverschmutzung Öl Ogoniland illegale Ölraffinerie (Getty Images/AFP/P. U. Ekpei)

Wani yanki da muhalli ya lalace a Najeriya

Kokari na amfana da albarkatun da Allah ya horewa Najeroiyar ta fanin alkintasu muhimmi ne, abin da Onarabul Ahmed Babba Kaita ya ce ita ce mafita da suka hango. Najeriya dai na cikin kasashen da basa daukar matakai na shawo kan sauyin yanayi duk da sanya hannu a yarjeniyoyi a matakin kasa da kasa. Ana dai fatan kafa doka zai taimaka wa farfado da aikin dasa shingen itatuwa a arewa da ma hanzarta kula da muhalli a yankin Niger Delta.

Sauti da bidiyo akan labarin