Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta kwato | Siyasa | DW | 04.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta kwato

Kamar yadda ta yi alkawari, gwamnatin Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta karbo daga hannun wadanda ake zargi da rub da ciki da dukiyar kasar.

Ministan yada labaru da al’adun gargajiya na Tarayyar Najeriyar ne Lai Muhammad, ya ce tsabar kudi sama da Naira miliyan dubu 78 ne da dalla milyan 185 da sama da dalla milyan 3 ne aka samu kwato wa daga hannun mutanen da ake zargin su da nuna halin bera a kan dukiyar kasa.

Gwamnatin ta samu kwato wadannan kudade ne daga ranar 29 ga watan mayun 2015 da ta karbi mulkin zuwa 29 ga watan Mayun wannan shekarar. To sai dai gwamnatin bata bayyana sunayen mutanen da ake zargi da rub da ciki a kan dukiyar Najeriyar ba, abin da shi ne a yanzu yafi daukan hankali al'ummar kasar.

Tuni dai kungiyoyi na fararen hulda da ke yaki da cin hanci da al'ummar kasar suka fara nuna jin dadinsu da wannan yunkuri da hukumomin na Najeriya suka yi wajen karbo kudin kasar da ake zargin an sace, sai da a share guda wasu na korafi dangane da gaza bayyana sunayen mutanen da aka karbe kudaden daga hannunsu.

Sauti da bidiyo akan labarin