1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Barikin Marte ya koma hannun soja

Abdoulaye Mamane Amadou
January 17, 2021

A yankin Arewa maso gabashin Najeriya, soja kasar sun sake kwato barikinsu na garin Marte da ya fada hannun kungiyar ISWAP mai da'awar jihadi a yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/3o23Q
Nigeria Boko Haram
Hoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

A cikin sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar, rundunar ta ce dakarunta na Opretion TURA TA KAI BANGO, sun fatattaki 'yan ta'addan tare da karbe iko da barikin garin mai iyaka da yankin Tafkin Chadi.

Sojan sun kuma tarwatsa motocin yakin mayakan kungiyar da dama, baya kashe da dama a yayin gumurzun da suka jima suna yi.

A yammacin Juma'ar da tagabata ce mayakan kungiyar Boko Haram reshen ISWAP suka kai farmaki a barikin soja da ke garin na Marte tare da karbe iko da barikin, lamarin da ya tilasta wa fararen hula da dama gudu don tisra da ransu a Maiduguri mai nisan kilo 130 daga yankin.