1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru uku ba Polio a Najeriya

August 22, 2019

Shekaru uku kenan rabon da a ji duriyar bullar kwayar cutar Polio a Tarayyar Najeriya da ta kwashi tsawon lokaci tana fafutukar ganin ta kare rayukan yara kanana daga bala'in kwayar cutar mai janyo nakasa.

https://p.dw.com/p/3OLRZ
Nigeria Polio Virus Impfung
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Wolfe

Alkaluma ya nuna cewa, Najeriyar ta taso daga kasar da ke kusan rabin cutar a duniya shekaru bakwai baya ya zuwa kasar da ta share shekaru uku ba tare da an sami bulla sabuwar cutar a tsakanin al'ummarta.Tun daga watan Augustan shekara ta 2016, kasar ta samu rahoton bullar cutar karshe a jihar Borno. Cigaba a cikin wannan hanya dai na nufin kasar na iya kai karshen annobar gaba daya tare da samun shedar Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya mai tasiri.


 Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar lafiya matakin farko da kawayenta da suka gina ingantaccen martani. Shugaban kasa nan take ya bada naira Miliyan dubu tara da dari takwas domin yakar cutar cikin kankanin lokaci. Sakamakon shi ne muke biki a yau shekaru uku ba tare da cutar shan inna ba nan da wattani shida masu zuwa, ana sa ran Hukumar Lafiya ta Duniya WHO za ta bai wa kasar shaidar kai karshen cutar in har ba'a sake samun bullar ta a ko'ina cikin kasar ba.

Nigeria Kinder
An kwashi shekaru ana fama da annobar cutar Polio a NajeriyaHoto: Imago Images/Zuma


Tuni dai sabuwar nasarar ta fara dadada ran 'yan kasar, kama daga masu dauke da cutar ya zuwa masu shugabantar  kungiyoyin fafutukar kai karshen cutar. Abun jira a gani dai na zaman iya dorewa cikin sabuwar nasarar dama dorawa zuwa gaba a cikin cututukan da ke zaman ruwan dare gama duniyar al'umma ta kasar.