Najeriya: Shekaru 60 da samun ′yanci | BATUTUWA | DW | 30.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Shekaru 60 da samun 'yanci

Shekaru 60 da samun 'yancin kai a Najeriya, sai dai za a iya cewa yankin Arewa maso Gabashin kasar ya kasance cikin koma baya a fannoni da dama, duk da tarin arziki da albarkatun kasa da yankin ke da su.

DW Still Boko Haram kill 65 people at funeral in Nigeria

Karuwar hare-haren ta'addanci a Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Gabas

Shekaru 11 ke nan dai ake fama da hare-haren kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar, ke taimakawa wajen dagula komai na ci-gaba a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar.

Karin Bayani: Makomar 'yan matan Chibok

Tun lokacin da yankin ke dunkule a matsayin jiha guda kawo lokacin da aka raba shi zuwa jihohi shida dai, a iya cewa an samu ci gaba ta fannonin kusantuwar gwamnati da al'umma da kuma wadatuwar cibiyoyin lafiya da manya gami da kananan makarantu, da suka saukakewa al'ummar yankin damar yin karatu. 

Karin Bayani: Kisan gillar ma'aikatan agaji a Najeriya.

To sai dai a sauran fannonin rayuwa a yankin ba su samu bunkasa yadda ya kamata ba, domin kuwa ba a iya amfani datarin arziki da ke kwance a cikinsa. A shekarun da su ka gabata, matsalar tsaro ta sake haifar da koma  baya ga dan guntun ci-gaba da ka samu a yankin, musamman ma a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa. 

Nigeria Maiduguri | Flucht vor Boko-Haram | Flüchtlingslager

Hare-haren ta'addanci, na tilasawa mutane kauracewa gidaje da garuruwansu

Ambasada Ahmed Umar Bolori jakadan zaman lafiya a Najeriya ne, a ganinsa duk ci-gaban da aka samu tun da ba zaman lafiya to ya zama na mai hakar rijiya. Ga masu fafutukar kare hakkin mata kamar A'ishatu Alhaji Kabu Damboa kuwa,

matan na daga cikin wadanda aka bari a  baya in ana maganar ci-gaba ne a  yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar.

Karin Bayani:

Dangane da tabarbarewa tsaro gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya ce an samu sauki kuma mutane su kara hakuri za a kawo karshen sa. Yanzu haka dai ana sa ran cewa yunkurin da gwamnonin yankin na Arewa maso Gabas, suka iya na hukuma da za ta mayar da hankali wajen bunkasa shi, al'amura za su sauya matukar aka aiwatar da abubuwan da aka yi nufi cikin gaskiya.

Sauti da bidiyo akan labarin