Najeriya: Sarkin Zazzau ya rasu | Labarai | DW | 20.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sarkin Zazzau ya rasu

Rahotanni daga jihar Kadunan Najeriya na cewa a yau Lahadi Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dr Shehu Idris rasuwa a wani asibiti da ke Kaduna bayan gajeruwar jinya.

Wani mai fada a ji a fadar basaraken ne ya tabbatar da rasuwar Dr Shehu Idris a yau Asabar 20.09.20, Alhaji Ibrahim Aminu wazirin Zazzau ya tabbatar da ya labarin rasuwar ya kuma ce nan gaba za a sanar da lokacin da za a yiwa marigayin jana'iza.

Basaraken dai ya shafe tsawon shekaru 45 yana kan gadon sarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a Najeriya, kana ya rasu yana da shekaru 84 a duniya ya kuma bar mata hudu da yara da jikoki.