Najeriya: Sankarau ta kashe sama da mutane 700
April 19, 2017Talla
Cutar da ake zargin ta Sankarau ce ta hallaka mutane 745 a Najeriya, adadin da ke zama karin kimanin mutane 250 a sama da mako guda kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana.
Sama da mutane 8,000 ne dai ake ganin sun harbu da kwayoyin cutar a fadin kasar kamar yadda aka samu rahotanni sama da watanni biyar. Kashi 93 cikin 100 na adadin sun fito daga jihohi biyar na Arewacin Najeriya. A makon da ya gabata dai adadin mutane da aka bayyana da rasuwa ta sanadin cutar sun kasance 489, mafi akasari yara abin da ya sanya shiga aikin rigakafin cutar ba kakkautawa. Jihohi biyar da annobar cutar ta Sankarau ta fi kamari dai na zama Zamfara da Sokoto da Katsina da Kebbi da Niger.