Najeriya: Rikici a zaben Bayelsa da Kogi | Labarai | DW | 16.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Rikici a zaben Bayelsa da Kogi

An fuskanci tashin hakali a zabukan gwamna da aka yi a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya da kuma Bayelsa a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Wahlen in Nigeria Warteschlange (AP)

Wakilin DW da ke yankin Niger Delta Muhammad Bello ya shaida mana cewar an samu tsaikon wajen fara zaben a wasu sassan jihar yayin da a wasu wuraren ciki kuwa har da Yenagoa babban birnin jihar, an yi harbe-harbe da samun satar akwatuna, batun da ya kai ga dakatar da zaben a wasu wuraren.

Can a jihar Kogi inda takara ta fi zafi tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da PDP da ke adawa ma dai an samu rahotanni na samun tashin hankali a wusu yankunan. Wakilinmu Ubale Musa da ke sanya idanu kan yadda lamura ke gudana a Kogi din ya ce an samu rahotanni na tada hankali da ma satar kuri'a a Lokoja, babban birnin jihar.

Tuni dai aka fara tattara sakamakon zaben daga matakin mazabu a jihohin na Bayelsa da Kogi kuma nan gaba ake sa ran mika shi ga kananan hukumomi kafin daga bisani a kai ga matakin jiha inda za a tattara sakamakon kana a bayyana wanda ya yi nasara a hukumance.