1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rage kudaden tallafi ga kungiyoyin jin kai a Najeriya

February 18, 2022

Ayyukan jin kai a shiyar arewa maso gabashin Najeriya na gab da shiga wani mawuyacin hali bayan da wasu kasashe da kungiyoyin da ke ba da tallafi domin yin ayyukan jin kai suka rage yawan kudaden da suke bayarwa.

https://p.dw.com/p/47GFs
Mun yi amfanin da wasu tsofin hotunan masu aikin jin kai
Mun yi amfanin da wasu tsofin hotunan masu aikin jin kaiHoto: Igor G. Barbero/MSF

Sannu a hankali ne dai kungiyoyin jin kan suka janye wasu ayyuka da suke gudanarwa a sassan arewa maso gabashin Najeriya inda matakin ya jefa dubban ‘yan gudun hijira da suka yi saura  ba a mayar da su garuruwan su ba cikin mawuyacin hali. A wasu sansanonin an kwashe watanni ba a samu taimakon agaji na abinci da ake musu na wata-wata ba kuma tuni da yawa daga cikin su,suka fada cikin matsalar yunwa kari bisa wadanda ake da su a baya. Wannan matsala za ta shafi dubban mutane da yanzu haka ke zaune a sansanonin da ba na hukumomi da ma wanda suke karkashin hukumomin da ke wasu yankuna da ba a rufe sansanoninsu ba. A ziyarar da na kai wasu daga cikin irin wadannan sansanoni na tarar babu wasu alamu na kungiyoyin jin kan da ke nuna suna aiki a wurin inda na tarar an rufe wasu cibiyoyin lafiya a wasu sasanonin. Malam Hashimu Musa wani dan gudun hijira da na tarar a sansanonin da ke Madinatu a Maiduguri ya bayyana min irin halin da su ke ciki bayan fara janye wasu daga cikin ayyukan kungiyoyin jin kan: ''Rabon da a ba da abinci a Madinatu yau sati goma sha biyu asibiti kuma da UNICEF take zuwa tana ba da magani it tace ta yi cilinic tana ba da magani a wajen UNICEF ta bar wurin fiye da shekara daya.''

'Yan gudun hijira a arewacin Najeriya cikin mawuyacin hali

Mosambik Ärzte ohne Grenzen in Cabo Delgado
Hoto: Igor G. Barbero/MSF

Akwai sansanin ‘yan gudun hijira da ake Kira Gubio Camp wanda ke karkashin kulawar hukumomi da mazauannan suka ce sun kwashe tsawon lokaci ba tare da sun ga masu kawo kayan agaji ba kuma ya zuwa yanzu ba a maganar mayar da su garuruwan su. A cewar Malam Baffa Musa wani mai aikin jin kai a sasanonin ‘yan gudun hijirar halin da ‘yan gdun hijirar ke ciki abun tausawa ne saboda ganin yadda wasun suke bin wasu hanyoyi masu cike da hadari wajen samun na sawa a bakin salati.