1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta samu nakasu a Najeriya

March 15, 2023

Bayan shafe shekaru ana fafutuka Najeriya ta hau hanyar kai karshen bala'in ta ta'addanci da ke komawa baya, rahoton wata kungiya da ke nazarin matsalar ta'addanci ya ce kasar ta yi nasara.

https://p.dw.com/p/4OhzR
Najeriya | Sojoji | Boko Haram
Sojojin Najeriya da makwabtanta sun jima suna fafatawa da kungiyar Boko HaramHoto: REUTERS

Rahoton dai ya ce Najeriya ta yi nasarar mayar da kungiyar Boko Haramun daga ta farko cikin batun ta'adda a duniya a shekara ta 2014, zuwa kungiyar da ba ta da tasiri a duniya a halin yanzu. Haka kuma rahoton da ke nuna girman ta'addanci a duniya dai, ya ce Tarayyar Najeriyar ta yi nasarar tashi daga matsayi na uku  a ta'addar a shekara ta 2015 ya zuwa na takwas a shekarar da ta gabata. Karin karfin soja da uwa uba sababbin makamai na zamani dai, na taka rawa a kokarin kai karshen matsalar da ta shafe shekaru da dauki suna na kasar ya zuwa laka. Sababbin jirage marasa matuka da kila ma dabarar lallashi a matakai na jihohi, a fadar Kabir Adamu na cibiyar Beacon Consult sun taka rawa wajen dakile batun ta'addar Boko ta Haram din.

Afirka | Najeriya | Matasa | Boko Haram | Tuba
Mafi yawan matasa da aka tilasta su shiga Boko Haram a Najeriya, sun tubaHoto: Ute Grabowsky/photothek/IMAGO

Daruruwan 'yan kungiyar ta BokoHaram din ne dai ke mika wuya kusan kullum, yayin kuma da tashin hankali ke kara lafawa a sassa dabam-dabam na yankin Arewa maso Gabas. To sai dai kuma in har kare ta'addancin Boko Haram din na shirin ya janyo  tsallen murna a bangaren 'yan mulki, ga Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya karin karfin ISWAP a cikin yankin na Arewa maso Gabas na nuna alamun jan aikin da ke gaban kasar a halin yanzu. Batun rashin tsaron dai, na zaman na kan gaba cikin jerin alkawuran da ke a tsakanin al'umma ta kasar da sabuwar gwamnatin da ke shirin hawa gado a Tarayyar Najeriyar.