Najeriya na son kwato bashin da ke kan ′yan kasuwa | Siyasa | DW | 26.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya na son kwato bashin da ke kan 'yan kasuwa

Hukumar da ke Kula da Bashi a Najeriya ta AMCON ta ce tsabar kudi akalla Tirilliyan biyar da Miliyan Dubu Dari Hudu na Nairai ne ke kan wasu 'yan kasuwa kasa da 300. Amma sun ki biyan bashin da ke kansu.

Hankalin Hukumar Karbar Bashin ta AMCON ya tashi saboda 'yan kasuwa da suka karbi bashi na cikin jiragen kansu a yayin da Najeriya ke cikin halin kaka- ni- ka yi saboda karancin kudi. Bankunan kasar da dama ne dai suka rushe sakamakon basuka na 'yan kasuwa da aka karba, amma aka ki biya duk da barazana ta hukumomin da ke da ruwa da tsaki da karbar bashin.

Ko bayan gaza karbo bashin da ke iya tasiri ga mahukuntan kasar da ke neman mafitar rikicin kudi ruwa a jallo, akwai tsoron yiwuwar durkushewar hukumar da dokar kafata ya bata damar kula da bashin da bai wuce Naira Milliyan Dubu 800 ba. Amma kuma ta samu kanta cikin rikicin da ke neman wucewa da saninta a yanzu.

Zentralbank von Nigeria

Babban Bankin Najeriya na fama da karancin kudi

Duk da cewar Najeriya ta yi nasarar kai da yawa a cikin manyan shugabanni na Bankuna zuwa gidan kaso, amma da dama daga 'yan bashin sun tsira sun kuma ci gaba da facaka da dukiyar al'umma cikin kasar. Kokarin sabobbin 'yan canjin na ambato sunayen 'yan bashin a jaridun kasar ya ci tura bayan barazana ta fuskantar shari'ar da ta biyo bayan matakin babban bankin kasar na CBN.

Ana dai kallon duk wani kokari na karbe kudaden na iya kaiwa ga karin barazana cikin harkoki na kasuwanci na kasar da ke tangal-tangal. Si dai kuma a tunanin Abubakar Ali da ke zaman masani ga harkokin kudin kasar, dabara na ga gwamnatin kasar na sauyi dabara da nufin tabbatar da karbe kudaden da ke iya tasiri ga makomar Najeriya.

Tsaka mai wuyar mahukuntan na Abuja na zaman karbe kudaden tare da jefa kasar cikin sabuwar barazana ta rusa kasuwa, da kuma kyale tare da aike sakon nunin fifiko a tsakanin masu kasuwa da masu siyasar da ke ji a jiki a halin yanzu.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos

Wasu masana na ganin cewar an karbo bashin ko ta halin kaka

Sai dai kuma a tunanin Mohammed Abubakar da ke zaman shugaban cibiyar Zero Tolerance on Corruption da ke zaman kanta a Abuja, babu wata mafita ga Hukumar ta AMCON face daukar duk matakan da suka wajaba da nufin karbe kudaden kasar da ke a hannu na kalilan.

'Yayan majalisar dattawan kNajeriya sun baiyyana aniyarsu ta taimaka wa hukumar da nufin jefa 'yan kasuwar kasar a cikin tsakiyar yaki da cin hancin da gwamnatin kasar ta sa a gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin