1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane miliyan 113 na cikin gararin karancin abinci

Abdoulaye Mamane Amadou
April 2, 2019

A cewar rahoton shekara-shekara na hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane miliyan 113 da ke rayuwa a kasashe 53 na duniya na fama da matsalar karancin abinci

https://p.dw.com/p/3G7Hl
Äthiopien | Sorghum & Papaya Farm
Hoto: DW/E. Bekele

 A wani rahoton hadin gwiwa da suka fitar a ranar Talata 02.04.19 hukumomin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya watau PAM da FAO  sun ce ana bukatar hada karfi da karfe daga ko'ina cikin duniya domin kawo dauki da agajin gagawa ga jama'ar da suke fuskantar matsalar.

Sauyin yanayi, da  matsalolin durkushewar tattalin arziki, da tashe-tashen hankula masu nasaba da yake-yake  da ma kaurar jama'a wadannan na daga cikin abubuwan da suka haddasa karancuin abinci.

Rahoton na shekara-shekara ya kuma  bayyana cewa kusan kashi biyu cikin uku na adadin mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa na rayuwa ne a kasashen Takwas ciki har da Afganista, Kwango, Habasha, Sudan Siriya Yamen da kuma Tarayyar Najeriya.

Haka zalika rahoton ya ce wasu sauran wasu kasasehen 17 da tun fil azal ke fama da matsalar yunwar na nan har yanzu bata sauya zane ba, kana kuma kasashe 13 ire-irensu Koriya ta Arewa, Venezeula ba su shiga cikin tsarin ba a wannan shekara saboda rashin cikakkun bayyanai.