Najeriya: Musulmi na Azumi cikin tsananin zafin rana
April 13, 2022Talla
Zafi wani yanayi ne da ke gigita al'umma, inda ake amfani da na'urar sanyi ko kuma fanka wajen rage radadinsa.
Sai dai a wannan lokacin da al'ummar musulmi ke yin azumin a bana, jama'a a jihar Adamawa musamman masu karamin karfi na kokawa.
Sai dai maluman addini na jan hankali tare da fadakarwa musamman ga masu azumin da su san cewa ibada suke yi.
A wannan yanayi na azumin bana dai jama'a da dama ne ke amfani da ruwan sanyi ko kankara a jikinsu domin rage zafin da suke ji.
Sai dai masana na danganta wannan yanayi da matsalar dumamar yanayi da gurgusowar hamada wanda suka ce ya zama dole gwamnati da al'umma su tashi tsaye yaki da sauyin yanayi.