1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sace-sacen jama'a yana kara tsamari

October 9, 2019

Duk dacewa hukumomi na ikirarin kokarin domin shawo kan matsalar a jihar Adamawa, garkuwa da mutane sai kara tsamari. Lamarin neman kudin fansa dai sannu a hankali yana kara ta'azzara musamman a arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Qxga
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

An soma satar mutane domin karban kudin fansa a yankin Niger Delta shekara 15 da suka gabata inda ake garkuwa da ma'aikatan kanfanonin hakan manfetur, sai dai yanzu wannan matsala ta game kasa baki daya.

Duk da cewar wasu naganin batun na garkuwa da jama'an, bata rasa nasaba da matsanaicin talauci, hada  da rashin aikin yi da ma shan miyagun kwayoyi da ke addabar al-umma.

Hukumomi dai na cewa suna kokarin don ganin sun sama wa matsalar ta satar mutane magani. Kakakin hukumar ta farin kya da ake kira Civil Defense, Chief Superintendent Suleiman Baba, ya tabbatar da faruwan wannan lamarin, da irin matakanda suke dauka a kai.