1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta soma yaki da dabi'ar yada labaran karya

Uwais Abubakar Idris
July 11, 2018

Najeriya ta kadammar da kamfe na yaki da labaran karya da kalaman batanci a kokarin shawo kan wannan matsala da ke kara rura wutar rikici ko barazana ga tsaro.

https://p.dw.com/p/31IA1
10 Jahre Hashtag
Hoto: picture-alliance/picturedesk.com/H. Fohringer

Kara tazarar yada labaran na karya da gangan bisa nufin tada fitina a tsakanin al'umma ne dai ya sanya gwamnatin Najeriya sanar da daukan wadannan matakai, domin gwamnatin ta ce irin wadannan labaran sun zama babban kalubale ga yanayin zaman lafiyar jama'a, inda suke bazuwa tamkar wutar daji saboda yawaitar wayoyi na tafi da gidanka da suka kai miliyan 150 a hannun jama'a da a ke amfanin da su wajen samun wadannan bayanai na karya da batanci.

Lai Mohammed Nigeria
Lai Mohammed ya ce, labaran karya sun haddasa asarar rayuka a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/S.Alamba

An tanadi dokokin hukunta masu yada labarun karya

Ministan yada labarai da al'adun Najeriyar, Lai Mohammed ya ce labaran karya tamkar bam ne da aka dana a kasar da ya sanya dole a dauki matakai, bisa la'kari da barnar da suke yi. Baya ga kadammar da kamfe da gwamnatin ta yi, akwai batu na amfani da dokokin da a ke dasu domin tabbatar da hukunta masu wannan laifi, abinda ya sanya shiga da jami'an tsaro a cikin lamarin.

Najeriya ta ce tana tattaunawa da manyan kamfanonin sada zumunta irin su shafin sada zumunta na Facebook da dandalin matambayi baya bata na Google don shawo kan matsalar, domin bayanai sun nuna cewa, wadannan kafafen da kansu sun dauki matakin na toshe kafofin da masu yada labaran karya ke bi su aikata barna ta hanyar kafofin sadarwarsu.