1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamun dan takarar shugaban kasa a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 5, 2019

Ana cigaba da tsokaci game da kamun Omoyele Sowore, shugaban kafar watsa labaran nan ta Intanet ta Sahara Reporters kuma tsohon dan takara a zaben shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar AAC mai adawa a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3NLUJ
Nigeria Sicherheitskräfte Boko Haram
Hoto: Reuters

Masu rajin kare hakkin dan Adam da 'yan siyasa na bangaren adawa a Najeriya sun yi tir da Allah wadai da kamun Omoyele Showore inda suke cewa yin hakan kokari ne na dankwafe 'yan adawa a Najeriya.

Masu aiko da rahotanni sun ce kamun na Sowore na da nasaba ne da wani kiran da ya yi na a gudanar da juyin juya hali a Najeriya.Tun a ranar da ya bayyana wannan fatan ne dai aka daina jin duriyarsa, sai a jiya Lahadi da jami'an tsaro sun ambata cewa ya shiga komarsu.