1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Majalisa ta amince da kasafin kudin 2020

Uwais Abubakar Idris AAI
December 5, 2019

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2020 wanda ta kasafta za’a kashe sama da Naira triliyan 10.594, abinda ya nuna kari a kan abinda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar masu.

https://p.dw.com/p/3UIE2
'Yan majalisar dattawan Najeriya
'Yan majalisar dattawan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Duk da raguwar da aka samu a kan kudadden da aka ware wa fanin aiyyukan yau da kullum na albashi domin jin dadin jami’ai, a kasafin kudin na badi ma wannan sashin ne ya samu kaso mafi tsoka, na sama da Naira tiriliyan 4.8, yayin da aka ware wa muhimman aiyyuka sama da Naira triliyan 2.4. Sanata Ahmed Babba Kaita na daga cikin 'yan majalisar datawan Najeriyar da suka yi wannan aiki.
‘Yan majalisar dai sun tsara kasasfin kudin a kan dalla 57 ga kowace gangar mai abinda ya nuna sun yi kari a kan abinda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar masu na dalla 55. Wannan ya sanya jimlar kasafin ya tashi daga Naira tiriliyan 10.33 zuwa tiriliyan 10.59. Ko mai yasa suka yi karin? Hon Muktar Aliyu Batara shi ne shugagan kwamitin kasafin kudi na majalisar wakila da wadanda suka amince da kasafin kudin.
Wannan ne karon farko da aka amince da kasafin kudin tun kafin shekara ta kare, domin kwanki 57 da gabatar da shi aka kai ga haka. To sai dai yadda aka yi muhawara ba tare da cikas ba ya bada mamaki, abinda ya sanya shugaban marasa rinjaye sanata Eyinaya Abaribe bayyana cewa.
Akwai ‘yan Najeriya da suka shiga majalisar don gane wa idanunsu. Mallam Abdullahi Garba a matsayin minista ya bayyana tunaninsa ga kasafin. An tsara kasafin kudin na Najeriya a badi a kan gibi na kashi 1.52 wanda bisa harsashe za’a aiwatar da shi ta hanyar ciwo bashi daga cikin kasar da kasashen ketare. A yanzu ya rage ga shugaban da ya dade yana ciwon bakin ‘yan majalisa ne ke hana shi yin aikinsa.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera