1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai sayar a kifi a jihar Kebbi

September 4, 2019

Wata matashiya jihar Kebbi ta watsar da girman kai ta rungumi sana'ar saye-da sayar da kifi bayan da ta kammala karatun ta na HND, ta ce sana'ar tata na samun tagomashi.

https://p.dw.com/p/3OzVl
Guinea Bissau Fischerei
Sana'ar sayar da kifi domin dogaro da kaiHoto: DW/B. Darame

Ita dai matashiyar mai suna Sadiya Usman da aka fi sani da Sasy ta ce ta shafe tsawon shekaru uku tana gudanar da wannan sana'a ta saye da sayar da kifin, inda take yin tattaki zuwa yankuna daban-daban da ake hada-hadar kamun kifi a jihar ta Kebbin kamar garin Yawuri da kuma Argungu, ta sayo danyen kifin tazo ta gasa ta kuma sassakashi cikin kwalaye tana sayarwa a jihohi daban-daban na Tarayyar ta Najeriya.

Matashiyar ta bayyana cewa sana'ar tata tasa tayi fice da kuma sadata da dimbin mutane da ko a mafarki ba ta taba sa ran haduwa dasu ba, amma kuma ta ce akwai kalubale, koda yake ta ce wadannan kalubalen da take fuskanta ba su sanya ta karaya ba, hasali sune suka kai ta  ga samun nasarorin rayuwa.