1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Magance rikicin manoma da makiyaya

Aliyu Muhammad Waziri
June 5, 2026

Sabon rikicin manoma da makiyaya ya haifar da asarar ran mutane goma sha daya a karamar hukumar Darazo tare da kona gidaje sama da dari da hamsin.

https://p.dw.com/p/5EwGw
Magance rikicin makiyaya a Najeriya
Magance rikicin makiyaya a NajeriyaHoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Rikicin ya faro ne daga inda wasu makiyaya suka kai farmaki kan wasu manoma a kauyen Lanzai da ke karkashin karamar hukumar ta Darazo yayin da suke aikin zuba taki a gonakinsu.

Magance rikicin makiyaya a Najeriya
Magance rikicin makiyaya a NajeriyaHoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Wannan shi ya fusata matasa daga garin na Lanzai suka je daukar fansa a kauyen Dosho inda fulanin suke da zama suka cinna wa gidaje wuta lamarin da ya kai ga asarar rayuka,

Da farko aka samu rashin mutune bakwai kafin daga bisani alkaluma suka gwada sha daya ne. Kan haka ne kuma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad y ace gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba.

Wani makiyayi a Najeriya yayin da yake kiwo da shanunsa
Wani makiyayi a Najeriya yayin da yake kiwo da shanunsaHoto: DW

Tuni dai rundunar yan sandan jihar Bauchin ta aika da jami'anta zuwa garuruwan na Lanzai, Dabo da Dosho domin tabbatar da zaman lafiya a yankin kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar Sani Omolori Aliyu ta bakin kakakin rundunar SP Nafi'u Habib.

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta ce jami'anta ba za su bar garuruwan da aka yi rikicin ba har sai komai ya koma daidai.