Najeriya: Legas ta dage komawa makaranta | Labarai | DW | 22.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Legas ta dage komawa makaranta

A wannan Litinin din ce dalibai a Najeriya suka koma makaranta amma jihar Legas a kudancin kasar ta dage komawar har sai 8 ga watan Oktoba don magance bazuwar Ebola.

Gwamnan jihar Babatunde Raji Fashola ya ce sun dau wannan matakin ne don ganin an kammala raba kaya na kiwon lafiya da kuma na kariya daga kamuwa cutar ta Ebola a makarantun da ke fadin jihar a wani yunkuri na ganin cutar ba ta cigaba da yaduwa ba.

Gabannin wannan matakin da gwamnatin ta Lagos ta dauka dai, kungiyar malaman makarantu ta kasar ta NUT ta nemi gwamnatin kasar ta kara hutun daliban don kimtsawa cif da nufin ganin sun tunkari wasu matsaloli ciki kuwa har da cutar ta Ebola sai dai gwamnatin ta yi watsi da wannan kira.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal