Najeriya: Kyautata yanayin shige da fice da dakile fataucin mutane | Siyasa | DW | 20.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kyautata yanayin shige da fice da dakile fataucin mutane

Najeriya ta kadammar da sabuwar manufar kula da shige da ficen baki a kasar da samar da sauye-sauye irinsu na farko a kasar, domin kyautata yanayin tsaro da dakile masu fataucin mutane.

Nigeria Abuja Migration Mohammed Babandede und Abdulrahman Dambazau (DW/Uwais Abubakar Idris)

Mohammed Babandede shugaban hukumar kula da shige da fice da Abdulrahman Dambazau ministan harkokin cikin gidan Najeriya

Wannan sabuwar manufa da Najeriyar ta bullo da ita na cike da sauye-sauye a kan wacce ake amfani da ita a baya, musamman kyautata yanayin tsaro da ma kokari na dakile matsalar kwararar baki daga Najeriyar zuwa kasashen duniya bisa hasashe na samun aljannar duniya da mahukunta suka ce babu ita.

Muhimman sauye-sauyen da ke cikin sabon tsarin a harakar kula da shige da ficen Najeriyar sun hada da bullo da dokar hukunta duk wanda aka kama da laifin safarar jama'a da a yanzu za a ci shi tarar Naira miliyan daya ko dauri na shekaru 10, da kuma  wajabta rijista ga duk bakon da ya shigo Najeriyar kuma zai kai kwanaki 90.

Karfafa guiwar masu shigowa Najeriya don kasuwanci

Ko ta wacce hanya wannan zai taimaka dakile matsala ta rashin tsaro da ake danganta ta da kwarar baki a kasar? Laftanan Janar Abdulrahman Bello Dambazau shi ne ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriyar ya yi karin haske.

"Abinda aka yi zai karfafa harkokin tsaro a kasa kuma ya bada damar wadanda suke da zummar shigowa Najeriya don kasuwanci su samu yin haka ba tare da wahala ba. Abubuwan da ke damunmu maganar ta'adanaci da shigowa da makamai da sauransu. Don haka duk wanda ya shigo kasar wannan tsari ya bada damar a san ina ya fito ina za shi kuma a ina ya zauna."

Niger Konvoi in Agadez (DW/A. Kriesch)

Rashin kwararan matakan kula da kan iyakoki a Afirka suna sa masu safarar mutane cin karensu babu babbaka

Bullo da sabon tsari na bayar da takardar izinin shiga Najeriya ga baki da za su shigo kasar domin kasuwanci a lokacin da suka iso tashar jiragen sama domin kawar da jinkiri da wahalhalun da suke fuskanta muhimmin sauyi ne a tsarin neman bisar zuwa Najeriyar. Mohammed Babandede shi ne shugaban hukumar kula da shige da ficen Najeriyar ya bayyana abinda ya sanya su daukan wannan mataki.

"Wannan ba mu kadai muke yin irinsa ba, akwai kasashen duniya da yawa da ke yi kamar Dubai, in ka je akwai inda za a ce ka zo ka karbi bisa. To mu abinda muke yi kafin ka baro gida domin zuwa Najeriya don harkar kasuwanci shi dan Najeriyar da za ka zo zai rubuta mana, in mun yi bincike za mu bashi bisa. Wannan sauki ne maimakon a ce sai mutum ya je ofishin jakadanci kafin yin hakan kaga an samu sauki."

Sabbin tsare-tsare na farko cikin shekaru barkatai

To sai dai dimbin sauye-sauyen da aka gudanar a wannan tsari da ke zama irinsu na farko a fiye da shekaru 50 a kasar, muhimmi ne ga Najeriya da ke fuskantar kalubale na kan iyakokinta da ke da fadin gaske, wanda ya wuce iko na sintiri ga jami'ai, har ila yau ga Mohammed Babandede.

"Wannan shi ne karon farko da aka yi sauyi a manufar kula shige da ficen baki a Najeriyar da tun 1964 rabon da a yi wannan."

Abin jira a gani shi ne tasirin da wannan zai yi ga taimaka kyautata al'amura na shigar baki da kuma kyautata yanayin tsaro musamman na ta'adanci da akan danganta shi da sulalar da baki ke yi zuwa kasar da manufa ta daban.

Sauti da bidiyo akan labarin