1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kutsen sojin Najeriya a cibiyar ‘yan jaridu da ke Borno

January 31, 2020

Ana ci gaba da yin Allah wadai da rundunar Sojojin Najeriya kan kutse da su ka yi a cibiyar ‘yan jaridu ta jihar Borno tare da kame wani mai aiki da jaridar Daily Trust.

https://p.dw.com/p/3X72D
Rundunar sojin Najeriya yayin kutse a cibiyar 'yan jarida
Rundunar sojin Najeriya yayin kutse a cibiyar 'yan jaridaHoto: Reinnier KAZE/AFP/Getty Images

Bayan sun kame Olatunji Omirin mai aiki da Jaridar Daily Trust sannan kuma suka saka masa ankwa abinda ake ganin neman tauye ‘yancin ‘yan jaridu ne. Kusan a iya cewa a ‘yan kwanakin nan ana yawan samun tsamin dangantaka tsakanin sojojin Najeriya da kuma manema labarai, musamman yadda manema labarai su ke bada rahotanni na koma baya da ake samu a harkokin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ko a jiya da yammaci, wasu sojoji cikin fararen kaya tare da rakiyar wasu sojojin cikin kayan sarki, dauke da muggan makamai sun afkawa ofishin ‘yan jaridu da ke Maiduguri inda su ka kame Olatunji Omirin tare da sa masa ankwa ba tare da bada wani dalili ba. Dukkanin kokarin da abokan aikin su ka yi domin ganin sun kwace shi daga hannun jami’an tsaron ya ci tura, saboda barazanar da sojojin su ka musu da makamai inda su ka tafi da shi zuwa bariki tare da yi masa tambayoyi.

Wasu daga cikin jaridun Najeriya
Wasu daga cikin jaridun NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo

Duk da cewa sojojin sun sako shi, bayan yi masa tambayoyi, kungiyar ‘yan jaridu da kuma kungiyoyin kare hakkin 'dan Adam da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai, har ma da talakawa sun yi Allah wadai da wannan mataki da suke ganin ana neman rufe gaskiyar abin da ke faruwa ne a yakin da ake yi da ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. Rundunar yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya wacce ake yi wa lakabi da 'Operation Lafiya Dole' ta  tabbatar da cewa an kama Olatunji Omirin kuma ba wani sabon abu ba ne jami’an tsaro su kama mutum domin neman bahasi kan wani abu.Manjo Janar Olusegun Adeniyi shi ne ya bayyana hakan, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a barikin Maimalari da ke Maiduguri.
''Ya ce an kama shi ne saboda wasu abubuwa da ake bukatar ya bada karin bayani akai. Ba a ci zarafinsa ba ta kowace hanya an kai   shi wani ofis ne inda ya rubuta bahasi. Amma mun sake shi daga baya. Saboda haka a Najeriya ba laifi ba ne a nemi mutum ya bada bayanai a kan wani abu da ake neman karin bayani”.
Wannan abin da sojojin su ka yi ya tada hankulan manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai, inda su ka bayyana takaicinsu dangane da abin da ya faru. Tuni dai kungiyoyin fararen hula da sauran al’umma suka nuna damuwa tare da yin Allah wadai kan wannan mataki na sojoji da suka ce ya sabawa tunani. A cewar Goni Sidi Mustapha Babankowa bai kamata ana samun rashin jituwa tsakanin manema labarai da jami’an tsaro ba musamman a wannan lokaci da ake neman samun sahihan bayanai na abinda ya ke faruwa a yaki da ta’addanci. Ko a shekarar da ta gabata ma dai rundunar sojojin ta kame wani ma’aikacin jaridar ta Daily Trust Usman Abubakar tare da rufe ofisoshinta a Maiduguri da Abuja, abin da ya sa masu fashin baki suka nemi a kawo karshen kame ‘yan jaridar ko ci musu zarafi, inda dimukuradiyya ta gaskiya ake son yi a kasar.