1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Umurnin kotu kan sakin editan jaridar Sahara Reporters

Gazali Abdou Tasawa
September 24, 2019

Wata kotun birnin Abuja a Najeriya ta umurci da a saki editan Jaridar Sahara Reporters ta saman intanet wato Omoyele Sowore bayan da ya kwashe kwanaki 45 a hannun hukuma. 

https://p.dw.com/p/3QBEX
Nigeria Omoyele Sowore
Hoto: CC by M. Nanabhay

Sai dai alkalin kotun Taiwo Taiwo wanda ya umurci hukumomin da ke tsare da dan jaridan mai adawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da su mika shi a hannun lauyansa, ya kuma umurci dan jaridan da dunga amsa kiran kotu a duk lokacin da ta kira shi domin shari'a. 

A farkon watan Agustan da ya gabata ne dai hukumar 'yan sanda ciki ta Tarayyar Najeriya ta shigar a gaban kotun kasar da takardar bukatar ci gaba da tsare editan jaridar ta Sahara Reporters mai shekaru 48, bayan da da ma ya kwashe kwanaki 90 a tsare.

Bukatar da kotun ta amince a wancan lokaci kafin a yau ta ba da umurnin sakinsa. Mahukuntan Najeriyan dai sun kama dan jaridan ne na bangaren adawa da ya yi fice wajen caccakar gwamnatin Shugaba Buhari bayan da a shafukan sada zumunta na zamani ya yi kira ga 'yan Najeriya da su fito su gudanar da juyin-juya hali a kasar.