1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sake salon magance matsalar manoma da makiyaya

February 5, 2020

A kokarin ganin karshen matsalar rikicin makiyaya da manoma a sassan Najeriya, kwararru sun yi wani zama inda suka yi nazarin mafitar rikicin da ke neman rikidewa zuwa rikici na kabilanci a wasu yankunan kasar.

https://p.dw.com/p/3XKIK
DW Fulani
Hoto: DW/K. Gänsler


Kwarraru  a cikin harkokin noma dana kiwo ne suka sun share tsawon yini guda suna nazarin matsalar da ta mamaye daukaci na sassan tarrayar Najeriya da ke neman ta gagari kundila. An turance dai an kallo sauyin yanayi da gwagwarmaya da yin tasiri a bangare guda biyun a matsayin ummul'abaisin annoba da ke zaman kan gaba cikin rigingimun kasar.

Manoma na fama da matsalar fili
Manoma na fama da matsalar filiHoto: Imago Images/photothek/T. Imo


Asalin matsalar dai ta faro tare da mamaye burtalolin kiwo a bangare na manoma sannan kuma ta abkawa gonaki ga masu sana'ar kiwon. Rikicin ne dai har ila yau ake yi wa kallon ummul'aba'isi na garkuwa da mutane bayan kare shanun da akai nasarar sacewa  a bangare na matasa na Fulanin.

Ya zuwa yanzu dai daukacin jihohin arewacin Najeriya sun amince da wani shirin a sake tsugunar da masu sana'ar kiwon a cikin neman rage cudanyar da ake yi wa kallon ummul'aba'isin rikicin mai hatsari. Najeriyar na tsakanin mai da sana'ar noma a gaban kowace ta zamani amma a  cikin rikici na rashin yarda da amincin al'umma daban daban.