1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance matsalar amfani da matasa a harkar tarzoma

Uwais Abubakar Idris MNA
October 8, 2021

An fara wani sabon kokari na shawo kan matsalar matasa zaune gari banza da almajirai da ke yawo a kan titunan Najeriya domin kalubalen da ke tattare da haka na tsoron amfani da su a aikata miyagun laifuffuka.

https://p.dw.com/p/41Sk0
Nigeria befreite Schüler in Katsina
Hoto: Afolabi Sotunde/Reuters

A Najeriya na fara wani sabon yunkuri da zumar shawo kan matsalar matasa zaune gari banza da ma yara almajirai da ke yawo a kan titunan kasar, domin kalubalen da ke tattare da haka na tsoron amfani da wannan rukuni na 'yan kasa a aikata miyagun laifuffuka na ta'adanci da ma masu garkuwa da jama'a da bayanai ke nuna suna daukan sabbin mambobinsu a Najeriya.

Kungiyoyin fara hula da ke fafutukar na nemo mafita daga wannan matsala da ma 'yan siyasa ne ke kokari na shaidawa juna gaskiya ta hanyar tunkarar mahukunta a kan matsalar ci gaba da samun matasa zaune gari banza a kusan dukkanin yankuna na Najeriyar, sannan ga yara almajirai da suke watangaririya da sunan karatu. Wadannan gungu na al'umma sun zama hanya mafi sauki ta shiga cikin kungiyoyin da ke aikata miyagun laifuffuka a Najeriyar.

A shekarun baya wasu gwamnatoci a Najeriya sun yi kokarin zamanantar da makarantun allo
A shekarun baya wasu gwamnatoci a Najeriya sun yi kokarin zamanantar da makarantun alloHoto: DW

Kwararru a harkar ilimi da dubarun mulki sun bayyana wannan matsala ta yaran da ke watangaririya da matsalar aikata miyagun laifuffuka na garkuwa da jama'a da ta'addanci a Najeriyar, musamman a daidai wannan lokaci.

Najeriyar dai ita ce kan gaba wajen yawan yaran da ba su zuwa makarantar boko da suka zarta milyan 10 a yanzu.

Ci gaba da yin biris na gaza daukar matakai na gaggawa a kan matasa zauna gari banza da almajirai da ke yawo a Najeriyar babbar barazana ce da kwararru suka ce kasar na zaune ne a kan bom da fara fashewarsa ne ake gani a matsalolin da suka addabi kasar.