1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro na kamari a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 8, 2021

Tabarbarewar al'amuran tsaro a Najeriya, na barazana ga fannoni da dama ciki kuwa har da fannin ilimi. A baya-bayan nan, mahara na kai farmaki tare da yin garkuwa da dalibai a Arewa maso Yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/3wFHv
Nigeria Kaduna | Entführung Schüler Bethel Baptist School
'Yan bindiga na yin awon gaba da dalibai da ke makarantun kwanaHoto: KEHINDE GBENGA/AFP

Al'amura na kara rincabewa a Tarayyar Najeriya, musamman a fannin tsaro. A baya-bayan nan dai, yankin Arewa maso Yamma ya bi sawun takwaransa na Arewa maso Gabas wajen fuskantar hare-hare daga masu dauke da makamai.

'Yan bindiga na shiga kauyuka a yankin na Arewa maso Yamma da ma Arewa ta Tsakiya, tare da yin harbin kan mai uwa da wabi. Su kan sace mutane da dabbobi da dukiyoyi, a wawasu lokutan kuma su kone gari ko kauyen da suka kai harin.

Ba wai a kauyuka kawai harin 'yan bindigar ya tsaya ba, su kan shiga makarantu su kwashe dalibai tare da neman kudin fansa. Ko da a makon nan mai karewa, 'yan bindigar sun kai hari a wata makaranta a jihar Kaduna inda suka kwashe dalibai tare da yin garkuwa da su, baya ga wani mummunan hari da suka kai a Katsina da ke makwabtaka da Kadunan inda suka halak mutane da dama.