Najeriya: Kare fararan hula a lokacin rikici | BATUTUWA | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Kare fararan hula a lokacin rikici

Kwararru a fannin tsaro karkashin cibiyar kula da mutanen da rikici ya rutsa da su a Najeriya, sun bayyana bukatar horas da jami’an tsaro a kan hanyoyin kare fararen hula a lokutan rigingimu ko yaki.

Nigeria Armee Anschlag in Abuja 25.6.2014 (REUTERS)

Sojojin Najeriya sun ja daga bisa titi domin bada tsaro

Karuwar adadin fararen hula da ake kashewa a dalilin rigingimu da ma yaki a Najeriyar dai, ya zama babbar matsala a yanzu, inda sannu a hankali ake neman raba dai-dai a adadin fararen hula da na masu kai hare-haren da ake kashewa a kasar, abinda ake dangatawa da yanayin da jami'an tsaro musamman sojoji ke tafiyar da kai hare-hare a yankunan da ake fama da rigingmu a kasar. Bincike ya nunar da cewa tura sojoji a jihohi da dama inda ake rigingimu na sanya kara kazancewar lamarin. Shin me ke haifar da hakan ne? Group Captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya masani ne a kan harkar tsaro da dabarun yaki kuma jami'i a  a cibiyar kula da fararen hula da ke cikin rikici a Najeriya:

Nigeria Anschlag in Gombe (picture-alliance/dpa)

Fararan hula da dama na mutuwa a lokacin rikici, ko yaki

"A da lokacin da muka tashi zaka ji an ce soja ya tafi bakin daga, bakin dagan nan wani daji ne ko kuma wani gari ne da babu kowa inda sojan wannan kasa da waccan kasa zasu hadu a gwabza, yanzu kuwa babu, Shi ya sa a binciken da aka yi aka gano cewa cikin yake-yaken da ake yi, in an kashe mutane goma to takwas zasu kasance fararen hula ne."

Ofishin jakadancin kasar Jamus dai na cikin wadanda suke tallafawa a kokarin tsara yadda za'a kare fararen hula daga rigingimu a Najeriya. Sai dai kuma a yayinda Dr Shambavi Goparkrishna Daraktar cibiyar kare fararen hula a hali na rigingimu ke bayyana fatansu na samun mafita, akwai bukatar hanzarta wayar da kan jami'an tsaro da fararen hular kansu don tsirar da rayukan wadanda basu da hannu a yakin amma yake rutsawa da su.

Sauti da bidiyo akan labarin