1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon tsarin gudanar da kudaden kananan hukumomi

May 7, 2019

A Najeriya gwamnatin tarayya ta dauki matakin karbe ikon gudanar da kudaden kananan hukumomi daga hannun jihohin kasar a wani yinkuri na kawo karshen mamayar kudaden kananan hukumomi da jihohin kasar suka jima suna yi.

https://p.dw.com/p/3I5M0
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Gwamnatin tarrayar ta ce daga yanzu babban laifi ne karkatar da kudade na kananan hukumomin zuwa jiha. Duk da cewar dai ana musu kallon daya a cikin matakai na gwamnatin tarrayar Najeriya guda Uku, ya zuwa yanzu dai mafi yawan hedikwatoci na kananan hukumomin tarrayar Najeriya sama da 774 ba su wuci kangaye da babu komai a cikinsu ba.

Wani hukuncin kotun kolin tarrayar Najeriya ne dai ya dauki ikon kula da kananan hukumomin ya mika ga jihohin tarrayar Najeriya 36. To sai dai kuma wani asusu na hadin gwiwa a tsakani na matakan guda Biyu, ya kare da komawa kafa ta wandaka a tsakani na jihohin da ke karbe kudaden da karkatar da su.Kafin wani sabon umarnin a bangaren hukumar kula da hada-hada ta kudade ta gwamnatin tarraya da ta ce tana shirin hukunta duk wani bakin da ya karkatar da kudade na kananan hukumomin domin duk wata manufa.

Nigeria Hauptstadt Lagos
Hoto: DW/C. Springer

Ana dai ana ta’allaka mafi yawan rikici na kasar da karkatar da kudaden da tun da farkon fari ke da babban burin samar da ayyukan raya kasa. Kazalika ana ta’allaka rigingimun rashin tsaro a sassa na kasar da wasashe kudaden da ya cancanci su kai ga kananan hukumomin a fadar Ibrahim Khalil da ke zaman shugaban kungiyar ma’aikata na kananan hukumomin tarrayar Najeriya ta Nulge. Dokokin tarrayar Najeriyar dai sun tanadi kaso 20.6 a matsayin kaso na kudade na kasar ga kananan hukumomin duk da cewar dai kusan kaso 60 cikin dari na al’umma na kasar na zaune cikin kananan hukumomin tarrayar Najeriya.