1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin malamai a makarantun bokon Najeriya

January 11, 2021

Duk da dubban malamai da ake yayewa kowace shekara a makarantun horar da malamai da jami'o'i a Najeriya, kasar na fama da karancin malamai.

https://p.dw.com/p/3nn5E
Nigeria - Lehrerin in Schule
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Langenstrassen

A tarayyar Najeriya duk da dubban malamai da ake yayewa kowace shekara a makarantun horar da malamai da jami'o'i a kasar, hukumar kula da ilimi daga tushe wato Universal Basic Education Commission a turance ta sanar da cewa akwai gibi na karancin malamai da alkaluma suka nuna cewa sun fi dubu 277 a harkokin samar da ilimi daga tushe.

A cewar masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi wannan matsala ta zama kadangaren bakin tulu ga hukumomi saboda yadda aka kasa magance karancin malaman duk da akwai da yawansu da ke gararamba su a neman aikin yi.

Karin bayani: Najeriya: Za a sake bude makarantu

A kowace shekara dai kwalejojin horar da malamai da jami'o'i a Najeriyar sukan yaye dubban malamai da ake zaton za su iya koyarwa a makarantun firamare da sakandare. Da dama sun cika da mamaki da jin cewa akwai gibi na malamai masu koyarwa a makarantun firamare da kananan makarantun sakandare duk dubban wadanda suka kammala makarantun horarwa da ke fadi tashin neman aikin koyarwa.

Nigeria l Schulstart - Schuleröffnung
Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba

Akwai malamai da suka watsar da aiki saboda samun wani aiki da kuma wadanda suka yi ritaya ko wadanda ta Allah ta kasance a kansu da aka dauki lokaci ba a iya cike guraben da suka bari ba, banda kuma karin makarantu da aka gina da ba a iya samar da malamai da za su koyar a cikinsu ba.

Ban da matsalar rashin daukar aiki da ake samu daga bangaren gwamnatin akwai kuma matsalar yadda wadanda suka kammala karatu a makaratun horar da malaman ke kin aikin koyarwa inda suke zabar wasu ayyuka da suke ganin sun fi samu.

Karin bayani: Daliban Najeriya za su yi jarrabawar WAEC

Wannan matsala na shafar kokarin da hukumomi ke yi na samar da ilimi ga miliyoyin yara a kasar da ma wadanda ake shirin haifa a nan gaba.

Nigeria Abuja 2014 | Studenten & Ergebnis der Prüfungen
Hoto: Imago Images/Xinhua Afrika

Yanzu haka dai wasu gwamnatocin jihohi sun fara daukar malamai domin cike wadannan gurabe, inda jihar Yobe da ke fama da kalubalen tsaro na Boko Haram, kungiyar da ke yaki da karatun zamani, take gaba wajen daukar karin malamai don cike guraben da ake da su.

Masana dai na kara jaddada cewa samar da ilimi ne kadai mafita ga dimbin matsaloli da ake fuskanta musamman a jihohin arewacin Najeriya kuma sai an samar da isassun malmai kafin a samu wannan biyan bukatar, abin da ya sa suke kira ga gwamnatocin jihohin kasar da su yi abin da ya dace.