Najeriya: Karancin fita zabe na barazana ga dimokradiyya | Siyasa | DW | 20.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Karancin fita zabe na barazana ga dimokradiyya

Rashin dandazon masu jefa kuri'u a zaben gwamnan jihar Anambara da aka kammala, ya haifar da shakku kan yadda lamarin zai shafi makomar siyasar Najeriya.

Salon mulkin dimokradiyya ana mashi taken "Mulkin jama'a domin jama'a," amma wannan na neman sauyawa a Najeriya. Inda duk da doki da aka san al'ummar kasar kan harkokin da suka shafi siyasa, amma kuma yawan mutanen da ke fitowa don jefa kuri'a na raguwa sosai.  Domin abinda ya faro kamar wasa daga 2014 a zabubbukan da aka yi na gwamnoni yanzu, ya kara bayyana a zaben da aka kamala na gwamnan jihar Anambara, inda cikin masu jefa kuri'u sama da miliyan biyu da aka yiwa rijista sama da mutane dubu 457 ne suka jefa kuria wanda ya nuna kashi 22 cikin 100 kenan.

Parlamentswahl in Lagos Nigeria NO FLASH (DW/Thomas Mösch)

Wasu 'yan Najeriya a layin kada kuri'un zabe

Kodayake duk da barazanar da kungiyar IPOB da ke ikirarin kafa kasar Biafra suka yi, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya a Najeriya na masu kashedin  nemo mafita daga matsalar.

A dai dai lokacin da aka kada kugen siyasa Najeriyar ke fuskantar zabubbuka a 2019, kwararru na bayyana bukatar kara jawo hankalin al'umma don sanin karfi na kuri'arka yancinka kada su bari baragurbi su sake darewa a matsayin shugabaninsu.