SiyasaAfirka
Jirgin ruwa ya nutse da fasinjoji a jihar Neja
May 26, 2021Talla
Fasinjoji kimanin dari da sittin jirgin ya dauko kafin ya nutse a tsakiyar ruwa bayan da aka ce jirgin ya dare gida biyu. Abdullahi Buhari Wara, wanda shi ne dagacin yankin Ngaski inda aka yi hadarin, ya ce kawo yanzu, mutum ashirin da biyu kadai aka yi nasarar ceto wa, an kuma gano gawar mutum guda, amma har yanzu ba su san inda saura, sama da dari suke ba.
Karin rahotanni na cewa, jirgin ya taso ne daga garin Minna da ke jihar ta Neja inda ya nufi jihar Kebbi da safiyar wannan Laraba, daga dai cikin fasinjojin sama da dari, akwai mata da yara kanana. Hadarin jirgin ruwa makamancin wannan, ana ci gaba da bincike da fatan gano sauran da ba a gani ba ya zuwa wannan lokacin.