1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda cikin farin kaya sun halaka masu bikin Easter

April 22, 2019

Wasu jami’an tsaro a jihar Gombe sanye da farin kaya sun halaka wasu matasa 6 da aka fi sani da ‘yan Boys Brigade bayan da suka take su da mota, akwai jami'ai biyu da su ma suka rasa rayukansu a sanadiyyar lamarin.

https://p.dw.com/p/3HD6z
Jami'an tsaro Najeriya lokacin da suke sintirin a daya daga cikin biranen kasar
Jami'an tsaro Najeriya lokacin da suke sintirin a daya daga cikin biranen kasarHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Lamarin ya auku ne a safiyar wannan Litinin a daidai lokacin da matasan ke zagayawa domin bikin murnar Easter. Matasan da suka yi jerin gwano kamar yadda suka saba yi a kowace shekara domin alamta bikin sun gamu da ajalinsu bayan da wasu mutane da ake zaton jami'an tsaro da ke tuki cikin yanayi na maye suka afka musu a kan titin sabon layi da ke jihar ta Gombe.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami'an tsaro sun fusata ne bayan da suka nemi wucewa da gaggawa inda dakarun kungiyar suka lalame su domin wucewa a hankali abin da ya bata musu rai suka juyo da mota tare da kashe wuta kafin suka kutsa cikin ayarin matasan. Nan take matasa shida suka mutu wasu kusan 26 suka sami munanan rauni kamar yadda Rev Adamu Dauda sakataren Gunduma na mabiya addinin kirista ya shaida wa wakilinmu Al-Amin Suleiman Mohammad.

Ya zuwa yanzu dai iyaye na tururuwa zuwa asibitin kwararru domin duba 'ya'yansu da wannan abu ya faru da su, inda kuma jami'an tsaro suka dauki matakai na kwantar da hankulan al'umma don gudun barekewar rikici.

Rev Adamu Dauda sakataren Gunduma na mabiya addinin kirista ya shawarci iyayen da suka rasa 'ya'yansu ko cikin wadanda suka jikata da su yi hakuri su kai zuciya nesa.

Kawo yanzu dai babu bayani daga bangaren jami'an tsaro ko gwamnatin jihar Gombe kan abin da ya faru da daukacin mutane suka amince da cewa ba harin ta'addanci ba ne.