1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Tsadar gas ta jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali

Uwais Abubakar Idris MNA
October 19, 2021

A Najeriya hauhawar farashin makamashin girki na iskar gas da ake fama da shi a kasar ta jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali, wasu sun koma ga amfani da itace da gawaki domin samun sauki.

https://p.dw.com/p/41sNW
Jemen Gaszylinder
Hoto: DW/J. Abdullah

Hauhawar farashin makamashin iskar gas da Najeriya ke fuskanta a yanzu da ke nuna sallamar ga kalubale da daukacin harkar makamashin ke fuskanta da aka fara gani a wannan fanni. Domin sunduki na iskar gas mai nauyin kilogram 12.5 da a baya bai wuce Naira dubu hudu ba yanzu ya kama hanyar kaiwa ga Naira dubu 10, kuma ba tsayawa lamarin ya yi ba, ci gaba ne ake yi na mai ginan rijiya.

Magidanta da ke amfani da makamashin iskar gas wajen girki sun kai ga kokawa a kan halin da ake ciki, domin kari ya zarta kashi 50 cikin 100 na kowane sunduki mai nauyin kilogram 12.5.

Matsalar kone gas cikin sararin samaniya ba bakon abu ba ne a Najeriya
Matsalar kone gas cikin sararin samaniya ba bakon abu ba ne a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Wannan na faruwa ne bayan da Najeriya ta amince da dokar sake fasalin daukacin harkar mai da iskar gas a Najeriyar, abin da ya hada da soke wasu ma'aikatu da suka shafi wannan harka. Amma ga Mallam Yusha'u Aliyu masani a fannin tattalin arziki ya ce farawa aka yi.

Alamu na yi wa masu amfani da makamashin iskar gas din dandana hauka, domin mata da yawa da suka yi sallama da hayaki na itacen girki da baya ga gurbata muhalli yake dalili na haifar masu da cututtuka, a yanzu dole kanwar na ki, ta sanya wasu komawa ga amfani da itace da gawayi.

A yayin da hauhawar farashin danyen mai da faduwar darajar Naira ke ci gaba da tasiri a farashin iskar gas a kasar, da alamu 'yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar wannan matsala har zuwa lokacin da za a gyara matatun man Najeriyar, wanda lokaci ne zai nuna hakan.