Najeriya: Harin bindiga a Anambra ya hallaka mutane da yawa | Labarai | DW | 06.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Harin bindiga a Anambra ya hallaka mutane da yawa

Da safiyar wannan Lahadin ce yayin da daruruwan jama'a ke harkokinsu na ibada, wasu mutane dauke da bindigogi suka buda musu wuta a Cocin Katolika na St. Philips da ke Ozubulu a jihar Anambra.

Hukumomi yankin sun sanar cewa mutane 11 ne suka mutu, sannan wasu 18 suka samu raunuka. Sai dai kuma wasu alkaluman da ba na hukumomin ba na cewa wadanda suka mutun sun kai kimanin 50 zuwa sama da 100. Gwamnatin jihar ta Anambra ta tattara kimanin likitoci 50 don bada kulawar gaggawa kan wadanda harbin 'yan bindigar ya rutsa da su, tare da alkawarin daukan nauyinsu. Sai dai kuma wasu da suka dubi lamarin na nuni da cewa harin na da nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin wasu 'yan uwan juna kan batu da ya shafi harkokin gudanar da wannan coci.