Najeriya: Halin rayuwar ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Halin rayuwar 'yan gudun hijira

Wata kungiya ta kasar Norway NRC ta ce wadanda yakin Boko Haram ya rutsa da su a yanki arewa maso gabashin Najeriya za a kwashe lokaci mai tsawo kusan gomai na shekaru suna bukatar agajin kasashen duniya.

A cikin wani rahoton da kungiyar ta NRC ta bayyana,ta ce a binciken da ta gudanar cikin wadanda suka fice daga gidajensu kusan mtum dubu 27 cikin miliyan daya da rabi. Kishi 86 cikin dari sun ce ba a shirye suke ba su sake koma a matsugunasu saboda abin da suka kira har yanzu na rashin tabbas a kan sha'anin tsaro.