Sabbin tsare-tsare a gidajen yarin Najeriya
August 15, 2019Wadannan sauye-sauye da aka sanar a kan harkar kula da fursunonin a gidajen yarin kasar sun biyo bayan rattaba hannu a gyaran fuskar da aka yi wa dokar da ta kafa wannan hukuma da shugaba Muhammadu Buhari ya yi. Sauye-sauyen da suka hada da sanya fursunonin su yi aiki a cikin al’umma da kuma daurin talala dukka da nufin gyara hallayensu.
An dai dade ana koke a kan halin da gidajen yarin Najeriyar suka shiga inda a kan tsare fursunoni da nufin gyara hallayensu amma sai su fito cike da munana dabi’un da suka koya wadanda gara ma kafin tsaresu. To sai dai tuni ana fara nuna damuwa a kan batu na kayan aiki da za’a iya aiwatar da wadannan sauye-sauye.
A ‘yan shekarun nan dai an ga sauye-sauye a hukumar gidajen yarin Najeriyar da ta bullo da tsarin karatu ga fursunonin inda wasu suka kai ga kammala digiri na digigir watau karatun dokta, da wadanda suka koyin sana’oi iri dabam-dabam.