Najeriya: Gwamnati ta nanata bukatar hadin kan kasa | BATUTUWA | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Gwamnati ta nanata bukatar hadin kan kasa

A yunkurinta na tabbatar da kwanciyar hankali a Najeriya gwamnatin kasar ta kaddamar da wani sabon shirin tattaunawa da bangarori na kasar da ke kartar kasar sai a raba cikin 'yan makonni.

Sannu a hankali dai karatun na shirin komawa na kwantar da hankula cikin tarrayar Najeriyar data kalli kari na tada hankali sakamakon kalamai na tsanar da suka mamaye sarari na samaniyar kasar. Kama daga 'ya'ya na kungiyar IPOB din dake neman sake ballewa da nufin tabbatar da kasar Biafra ya zuwa matasa na arewan da suka mika wa'adi na daya ga watan Oktoban dake tafe dai al'amura na kara nuna alamun lalacewa a cikin tarrayar Najeriya a halin yanzu.

Sai dai kuma a kokari na neman mafita da yammacin wannan Talata gwamnatin kasar ta kaddamar da jerin tattaunawa da bangarori daban daban cikin kasar da nufin nazari na korafi da ma neman mafitar matsalar. Ya zuwa yammacin shugaban kasar dake riko Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wata ganawa da dattawan arewacin kasar bisa jagorancin kungiyar dattawan ACF da sauran masu ruwa da tsaki da harkokin addinan kasar biyu dama kafafen labarai a arewar. Karkashin ganawar dai kuma a fadar Osinbajon, gwamnatin na fatan jin matsalolin kowa tare da dauka na matakan kaiwa ga zama na lafiya tsakanin kowa. Gwamnatin kasar dai a fadar Osinbajon ba ta da niyyar lamuntar duk wani kalami na tayar da hankali komai kankantarsa.

"Yanzu ba lokaci bane na buya a karkashin kalamai na tsana. Lokaci irin wannan ba na ware kai bane. Ina son rokon ku dake nan dama daukacin al'umar tarrayar Najeriya cewar fa lokaci ne na aiki tare. A matsayinmu na gwamnati a shirye muke mu tabbatar da hadin kan kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar. Kuma ina son in tabbatar cewar kalamai na tsana ko raba kai inda ya ke na haramun to zai fuskanci karfin doka. Babu wata tababa game da kudurin gwamnati na ganin cewar ba a kyale wani ya sha da kalaman da zasu kawo rabuwa, ko tada hankali."

Osinbajon dai ya yi kalaman nasa ne a kewaye da manyan shugabannin jami'an 'yan sanda da hukumar tsaron cikin gida na DSS dama babban hafsa na tsaron tarrayar Najeriyar, a wani abun dake zaman alamun aiken sako na shirin gwamnatin na fitowa fili wajen murkushe kokari na tada hankalin.

Ana dai sa ran kowane a cikin mahalarta taron zai samu dama ta fadar ra'ayinsa kafin daga baya gobe gwamnatin kasar ta gana da 'yan uwansu dake sashen kudu maso gabashin kasar. A ranar Juma'a da kuma Lahadi dai an kuma tsara Osinbajon zai gana da sarakuna a sashen na kudu da arewa, duk dai cikin karatun ba hanyar araba din dake dada girma a idanu na gwamnatin. Babban tsoron gwamnatin dai a fadar osinbajon shi ne duk wani surutu na tsana na iya karewa tare da lahani na wadanda ba su ji ba balle su gani cikin kasar da kila ma a wajenta.

Akwai dai fatan sabon yunkurin na iya kaiwa ga kwantar da hankula da ma kila mai da wukar cikin kube a tarrayar Najeriyar da ke fata na ficewa a cikin rikicin rashin tsaro amma kuma ke tunkarar wani babu shiri.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin